BARKA DA ZUWA SHAFI MAI ALBARKA
Alhamdulillah muna muku albishir insha Allah zamu dawo aiki gadan gadan!Tambayoyi da amsarsu tare da
Mallam Ibrahim Zakzaky na ashirin da tara
Shin da gaske Musulunci zai kasu kashi 73?
TAMBAYA: Assalamu alaikum. Allah ya gafarta Malam, ina neman karin haske game da hadisin nan da ke cewa wai Manzo Allah (S) ya ce addini zai kasu kashi 73. A nan Manzon Allah yana nufin akidu ne kamar a ce Izala, Darikar Tijjaniyya, Shi'a, Kadiriyya da sauransu, ko kuwa ya abin yake ne?
Daga Amina M. Ahmad Dankwaro dankwaro2005@yahoo.com
SHAIKH ZAKZAKY: Lalle babu wani hadisi da ya ce addini zai kasu kashi-kashi. Addini yana nan kashi daya, tun lokacin da wannan Manzo (S) ya zo da shi, har ya zuwa kuma ranar karshe, addini yana nan kashi daya. Amma fitina za ta zo wadda za ta rarraba al'umma ya zuwa kashi 73. Abin da hadisin ya nuna kenan. Al'umma ce fitina zai same ta, ta rarrabu, ba wai addini ne shi a kan kansa zai kasu kashi-kashi ba. Saboda haka idan ya lura da kyau zai ga akwai bambanci tsakanin al'umma ta rabu da addini ya rarrabu. Shi addini ba zai rarrabu ba, amma al'umma, muna iya ganin yadda fitintinu suke ta zuwa mata suna rarrabuwa, amma rarrabuwar nan 'fima labudda' ba yana nufin kungiyoyi ne wadanda akan yi su da kyawawan manufofi, ko makarantu. In wadannan ne yanzu idan kana lissafinsu za ka iya samun ma miliyoyi, ba 70 ba. Abin da ake nufi (al'umma) za su rarrabu ne a kan su bar addinin, su zama kungiyoyi, amma guda daya rak za ta kasance take a kan addinin. Ko ba ka lura ba. Amma su duk cikarsu sunansu al'umma Musulma, amma ba su yi 'tamassuki' da addini din ba. Kuma tunda yake hadisin haka ya zo da shi, bai ce mana da su wane, da su wane, da su wane ne ba, saboda haka kullum sai ka yi kokari ka ga cewa kai a wanne kake? Kana tare da al'umma ne wacce take rike da 'hablullahil matin' ko kuwa? Allah kuma ya kiyaye mu wannan fitinar.
TAMBAYA: Assalamu alaikum. Malam wai meye hukuncin Malaman makarantun boko musammaan na Jami'a da suke kayar da dalibansu a jarabawa bayan kuma a gaskiyance sun ci jarabawar tasu?
Daga Sani Yaro saniyr@yahoo.com
SHAIKH ZAKZAKY: Tunda shi 'ma'anuni' ne a kan cewa zai yi gaskiya tsakaninsa da Allah, in mutum ya ci ya ce ya ci, sai ya ci ya ce bai ci ba, ka ga ya ci amana kenan, kuma za a tambaye shi gobe kiyama, ko da ba a gano shi ba a nan duniya.
TAMBAYA: Assalamu alaikum. Malam, idan na kalli mace musulma na kau da kai, amma kuma sai na ga mata wadanda ba musulmi ba sun yi tabbaruji, yaya zan yi kenan?
Daga Lawal Na Kabiru Zuba Abuja 0803 594 1531
SHAIKH ZAKZAKY: Duk ana kawar da kai ne, muminai suke, ko kafirai. Sai dai ana cewa su kafirai idan sun takaita ya zuwa shigarsu ta al'ada, ba 'tabarruji' ba, kamar ga shi ba su hijabi irin na musulmi, amma ga shi sun yi shiga irin wanda ake sa wa a al'adance a suturce al'aura, ba laifi da mu'amala da su har da kallon su, amma ba 'ribatan' ba. Ba kallo 'ribatan' ba, ba kallo da sa sha'awa ba. Idan dai kawai kamar kallo na ciniki ne, ko na magana, alhali ba su sa hijabi ba, babu laifi. Kuma har ila yau ma ana cewa ana riskar da ma matan musulmi da wannan hukunci din, idan ya zama su matan musulmin misali ba su lizimtar hijabi, ko an ce masu su yi, ba sa yi, kamar irin matan kauyuka, wadanda ba su faya sa hijabi ba, kuma ko an ce su sa ma, ba za su sa ba. Su ma ana riskar da su da wannan hukuncin. Ala'ayi halin, a duk wadannan ba a ce a kalle su da kallon sha'awa ba. Kuma idan suka bayyana tsiraici kamar fatar jiki, ko suka sanya tufafin da ya matsi jiki da ya nuna siffa, to shi wannan bai shiga ciki ba.
TAMBAYA: Assalamu alaikum. Malam zan iya kiran wanda ba shi ya haifi ni ba, Baba?
Daga Lawal Mai Kaji Bauci
SHAIKH ZAKZAKY: Kalmar Baba na iya nufin girmamawa, ko da mutum ba mahaifinka bane, yana nufin kana girmama shi kamar matsayin Babanka. Ba lale ne yana nufin Mahaifinka ba. Amma idan ka ce wane, shi ne ubanka, mahaifinka, to wannan dole ya zama shi ne ya haife ka din kenan.
TAMBAYA: Assalamu alaikum. Malam akwai masu cewa duk wani halin kuncin da ya samu mutum daga Allah ne? Shin hakan ne kuwa?
Daga Lawal Mai Kaji Bauci 0804 502 7079
SHAIKH ZAKZAKY: Idan ya yi wa abin kyakkyawar fassara ba mummunar fassara ba, sai a ce haka ne. Kamar da misali sai ya sa kansa a cikin wani hali, sai ya ce Allah ya sa shi, to ya yi masa mummunar fassara kenan. Amma kyakkyawar fassara ita ce, komai yana hannun Allah ne, kunci da wadata, kuma wajensa ake neman mafita, gare shi kuma ake godiya a yayin wadata. Wannan kyakkyawar fassara ce. Sai mu ce haka ne. Bai kamata ya shigar da kansa wani hali ba, ya zo kuma ya zargi Allah.
TAMBAYA: Assalamu alaikum. Malam ya halatta mutum ya nuna ba ya son 'ya'ya mata sai maza?
Daga Shehu Idirs Buni Yadi a jihar Borno
SHAIKH ZAKZAKY: Tana iya yiwuwa shi ya fi son 'ya'ya maza din ne, amma dai ba zai zama daidai ba in zai kyamaci mata din ne, ko ya nuna masu bambanci don su mata ne, shi zai zama mummunan abu. Amma idan a al'adar ransa ne ya zama shi ya fi son ya haifi namiji, masalan, wannan za a ce babu laifi da shi.
TAMBAYA: Assalamu alaikum. Malam ana iya ajiye zakkar kayan noma zuwa wata shida sannan a fitar da ita?
Daga Shehu Idirs Buni Yadi a jihar Borno
SHAIKH ZAKZAKY: Bai halatta a jinkirta zakka ba, daga lokacinta. Allah (T) yana cewa a ba da hakkinsa ranar girbinsa, saboda haka, tun ranar da ka girbe, ya zama ka cire naka, tun ran nan kuma shi fakiri za a ba shi nasa hakkin. Saboda haka, in ka yi jinkiri da shi ka aikata haram, duk da dai bai fadi a kanka ba.
TAMBAYA: Assalamu alaikum. Malam ya irin mutanen da Allah ke halitar su da al'aurar maza da mata za su yi idan sun kasance a cikin 'yan uwansu na jini. Idan an zo rabon gado wane rabo za su dauka? Na mata za a ba su, ko na maza?
Dag Muhammad Sani Minna jihar Neja 0803 649 6729
SHAIKH ZAKZAKY: Akwai wanda ake cewa 'hunsa' mai al'aura biyu. Akwai kuma wanda ake ce masa 'mushkil,' wato wanda yake da mishkila, wanda aka kasa tantance namiji ne shi, ko mace. Saboda haka iri biyu ne. Akwai 'hunsa' wanda yake ba 'mushkil' ba, akwai kuma 'mushkil.' Idan 'hunsa' ne ba 'mushkil' ba, za a yi masa hukuncin wanda ya rinjaya. Wato zai zama namiji ne shi, ko mace. Duk wanda ya yi rinjaye. 'Mushkil' shi ne wanda aka kasa rinjayarwa, wanda shi a rabon gado an nuna ana ba shi rabin kason kowanne ne daga ciki. 'Mushkil' kenan, rabin kason kowanne daga ciki kenan za a ba shi.
TAMBAYA: Allah ya gafarta Malam, a cikin Mafatihu a ayyukan Yaumul Bi'ith, akwai wani hadisi, inda aka tambayi Imam Ja'afar As-Sadak (AS) game da yi ko sauraron waka a daren ko a ranar Juma'a, sai ya nuna kamar ba shi da kyau, amma ni kuma na ga mukan shirya majalisi a irin wannan lokacin? Wane karin haske Malam za a yi min game da haka?
Daga Abdulrasheed Daudauwa jihar Katsina
SHAIKH ZAKZAKY: Kodayake mun taba amsa wata tambaya mai kama da wannan. Amma yadda ya zo ba shi da wata alaka da Yaumul 'Bi'itha.'An nuna cewa yin wake a daren Juma'a ne bai kamata ba. Wato ka ga kenan wannan yana daga cikin koyarwar mutum ya shagalta a wadannan darare masu daraja da ayyuka da zai samu lada mai yawa, ba domin shi wake din na halas din ya haramta ne a daren Juma'a ba, sai dai tunda yake akwai ayyukan lada masu yawa da mutum ya kamata ya shagalta da yin su a daren Juma'a, to bai kamata ya zama maimakon su yana yin wasu ba. Dama wannan bayanin mun taba yin sa a baya.
TAMBAYA: Assalmu alaikum. Malam idan mutum yana neman aure yana ba da kyaututtuka a gidan iyayen yarinyar da yake neman, amma ba a matsayin sadaki ba, sai dai don kyautatawa. Shin idan bai samu auren yarinyar ba, zai iya neman a biya shi wadannan kyaututtukan da ya bayar?
Daga Abdulrasheed Daudauwa jihar Katsina
SHAIKH ZAKZAKY: Shi da kansa ya ce kyautatawa ne. Da ya ce a matsayin sharadin aure ne, ko da ba sadaki bane, to da sai a ce yana iya cewa a ba shi, tunda an shardanta masa ne a kan a ba shi wannan kyautar a ba shi mata. Amma kuma ba a ce masa sadaki ba. To amma tunda shi da kansa ya ce a matsayin kyautatawa ne, ai ka ga ba zai kyautata ya dawo ya munana ba.
TAMBAYA: Assalamu alaikum. Malam na ji an ce duk abin da mutum ya aikata a nan duniya sai ya rubuta shi a kabari. Har da laifin da mutum ya tuba zai rubuta, ko kuwa?
Daga Muhammad Salisu Minna jihar Neja
SHAIKH ZAKZAKY: Ba ana nufin mutum ne zai rubuta, a ba shi alkalami da takarda ya yi ta faman rubutu ba. Abin da dai muka sani shi ne, Allah ya wakilta wa kowane bawansa Mala'iku masu rubuta ayyukansa, mai kyau, ko marar kyau, kuma ranar alkiyama za a mika masa takardunsa dauke da wannan, kuma zai karanta, 'sawa'un' za a yafe masa, ko kuma za a yi masa azaba, duk dai zai gan shi a rubuce, sannan in za a yafe masa kuma a yafe masa. Wannan abin da muka sani kenan. Akwai kuma ruwayar da ke cewa shi mai rubuta zunubi yana karkashin mai rubuta lada ne, saboda haka ba zai rubuta ba, sai mai rubuta ladan ya ce masa, "to rubuta." In ya aikata laifi, sai ya ce a saurara masa, kila ya tuba a share masa. Sai ya zama ba a rubuta ba. Ka ga wannan kenan ya nuna abin da ya aikta wanda aka yafe, ba ma zai gan shi ba kenan.
TAMBAYA: Assalamu alaikum. Malam mutum zai iya shiga i'itikafi a ran 19 ga watan Ramadan, kuma ya fito a ran 29 ga watan Ramadan?
Daga Saleh Shehu Yadin Lere, jihar Kaduna.
SHAIKH ZAKZAKY: Ka'idar i'itikafi dai shi ne, duk lokacin da ya kwana biyu, to kwana na uku zai ayyanu, saboda haka yana iya yin kwana 10 kenan, amma in har ya yi na 11 to na 12 zai zama lazim. Duk lokacin da ya yi kwana biyu, sai ya kawo na ukun. Wannan kuma bayan ukun farko kenan, tunda a wurinmu ba zai iya yin i'itikafi kasa da kwana uku ba. Bayan kwana ukun farko, duk lokacin da yi kwana biyu, to na uku ya ayyana. Nan kamar yadda ya ce, ya shiga 19 ya fita 29, ka ga ba ya sami kwana 10 ba? Ka ga zai iya yin kwana 10. Amma da zai yi 11 ne, da sai ya zama sai ya kara na 12. Da takwas ya yi, da dole sai ya yi na tara. Ka fahimta ai? Amma in ya yi 10 ba a ce sai ya yi na 12 ba. Duk lokacin da ya yi biyu, sai na uku.
TAMBAYA: Assalamu alaikum. Malam ina hukuncin mutumin da ya yi rihi (tusa) a cikin salla, amma sai ya ki ya fita daga masallacin, sai ya ci gaba da kwatanta kamar yana salla saboda kada ya fita ya bar mutane cikin shakku? Daga Abdurasheed Daudawa jihar Katsina
SHAIKH ZAKZAKY: Ba haka nan zai yi ba. Tunda ita salla ba ta inganta ba alwala, saboda haka bai halatta masa ya ci gaba da kwatanta salla, alhali ba salla yake yi ba. Abin da ya kamata ya yi shi ne, ya fita. Akwai wasu 'Fukaha' da suka ba da wata dabara ta cewa; sai ya kama hancinsa kamar ya yi habo ne. Kuma shi ma wannan dai hikima ce. Wato kenan sai mutane su dauka jini ne ya shiga gangaro masa, shi ya sa ya fita waje. Kodayake ba haka bane, sai ya je ya sake alwalarsa ya dawo, in ya samu ma ana nan ana salla din, sai ya bi ya samu jam'i na dan abin da ya saura, in ya samu kamar ko da raka'ar karshe ne, misali. Amma batun cewa in ya fita zai sa wa mutane shakku, wannan bai taso ba. Shakku na mene? Saboda sallarsa ai ba ta shafi wani ba, ballantana a ceЕ Yana shakkun mene da zai faru? Lalle wannan dai ba daidai ne ba, ya yi salla ba shi da alwala. Bilhasali ma ya haramta masa ya yi salla ba alwala. Saboda haka wajibinsa ne ya yanke sallar ya fita, sai dai wannan dabara din ta toshe hanci, za ta nuna cewa ba wani abin kunya bane, habo ne ya gangaro. Kodayake bai zama dole ba, ko da ya fita, ai mutum yake shi, kuma abin da ke bijiro wa dan Adam, yana iya bijiro masa.
TAMBAYA: Assalamu alaikum. Malam wasu suna cewa idan mutum ya tara da matarsa a dakin da yake akwai yaro karami ko da yana barci ne, sai yaron ya zama fasiki. Ya wannan yake a mazhabar Ahlul Baiti? Idan kuma haka ne, ya mutum zai yi kenan da yake ana cikin wani hali a wannan kasar ta yadda mutum yake kwana da matarsa a daki daya da kuma yara da yawa.
Daga Abdulrasheed Daudawa Katsina 0805 471 0211
SHAIKH ZAKZAKY: Abin da dai aka sani haramun ne yin jima'i tare da yaron da yake iya hankalta, ko da kuwa yana barci ne. Yaron kuma ana cewa kamar daga dan shekara biyu zuwa sama, in zai iya fahimtar abubuwa, amma idan kamar mai shan nono ne, babu laifi da wannan.
TAMBAYA: Assalamu alaikum. Malam ana neman taimako ne na gina masallacin Juma'a sai kwamitin neman taimakon ya ce mutum zai iya ba da zakkar amfanin gonarsa ga masallacin. Shin Malam hakan yana iya halatta?
Daga Hamza Idiris Iliya Gombe
SHAIKH ZAKZAKY: Ana iya cewa eh, ta fuskacin fisabilillah, don ana cewa kason fisabilillah yana zama duk wani abu domin amfanin al'umma. Amma wannan sai idan babu fakirai mabukata, sannan za a je ga haka nan. Amma idan akwai fakirai mabukata, sune suka fi cancanta, fiye da gina masallaci, ko makaranta, ko abin da ya yi kama da haka nan.
TAMBAYA: Assalamu alaikum. Da yake Malam ya fadi hukuncin yadda za a yi idan mutum ya tafi ya bar gida bai dawo ba har na wani lokaci. To Malam idan mutum din ya tafi kuma sai aka fid da ran ba zai dawo ba, sai bayan matarsa ta auri wani, 'ya'yansa sun raba gado har ma wasu sun sayar wa wasu nasu kason da suka samu, sai kuma wannan mutumin ya dawo. Ya za a yi kenan?
Daga Muhammad Ango Dosara jihar Zamfara
SHAIKH ZAKZAKY: Ban san ko har na ba shi labarin rabon gado ba? Kila shi ne ya kara da rabon gado, domin kuwa hukuncin 'mafkudi' daban yake kuma da rabon gado. Batun hukuncin aure na hukuncin 'mafkudi' daban yake da rabon gado. Na aure ana cewa bayan shekara hudu ne ana cigiya, to sannan za a yarje mata ta yi idda, idan ta gama idda, sannan tana iya aure. Shi kuwa rabon gado ba a ce za a yi shi nan take ba. Sai an masa mikidarin shekara 70 daga lokacin haihuwarsa, to sannan ne ake iya raba gado. Saboda haka ka ga hukuncin aure ya bambanta da na gado. Kuma in ya zama duk an yi wadannan duk, sai mutum ya dawo, falillahilhamdu, amma waccan maganar an riga an gama. Matar ta riga ra yi aurenta, shi kenan alhamdulillahi ba wata magana. Kuma gadonsa an riga an ci alhamdulillahi, kuma alhamdulillahi yanzu da ya dawo.
Don haka idan an ce ta yi aure, ba ana nufin kuma a raba gado bane. Shi rabon gadon hukuncinsa daban ne. Shi sai an kiyasta ya shekara 70 daga lokacin da aka haife shi, ba daga lokacin da ya bar gida ba, in an ga cewa bayan shekara 70, to shi kenan ana iya raba gadonsa. In ya dawo kuma falillahilhamdu. Amma dai wannan ya riga ya wuce, ba sai a dawo masa da kayansa, ko a dawo masa da matarsa ba, yanzu ya riga ya wuce. TAMBAYA: Assalamu alaikum. Malam idan za a kai gawa makabarta a gaban mutane ya kamata ta kasance, ko kuwa a baya?
Daga Ashiru Salisu Babbar Riga
SHAIKH ZAKZAKY: Wasu suna cewa ya kamata wasu su yi gaba ne kadan, wasu kuma su yi baya. Sai ya zama akwai mutane a baya, akwai kuma mutane a gaba. Amma abin sani dai ana sa shi a gaba ne. Sai dai akwai masu cewa ya kamata wasu su riga shi zuwa kabari din, don ya zama kamar ba an kai shi da sigar girmamawa bane, an je da shi ne da sigar ana nema masa rahama ne.
A cikin 'adab' ladubban raka gawa kabari, akwai cewa ana sa gawar a gaba ne a bi ta. Amma akwai masu cewa tunda ana nema masa rahama ne, kar a nuna shi a gaba tamkar ana girmama shi, sai wasu su riga shi zuwa kabarin, su wuce gaba kenan, da fatan su je su fara addu'a kafin a iso da shi.
TAMBAYA: Assalamu alaikum. Malam wani dan uwa ne yake da 'ya da ta isa aure, sai wani dan uwan ya nuna yana son ta zai aura, bayan an yi duk binciken da ya kamata, an gamsu da shi, ita ma yariyar ta amince da shi, sai uban wannan dan uwan (Mahaifin yarinyar) ya ce, bai yarda wannan dan uwan ya auri wannan 'yar ba, saboda ya bincika ya gano shi dan Shi'a ne, amma sai uban yarinyar ya yi kokarin ya gamsar da shi, amma ya ki gamsuwa, wannan ya kai ga ya haifar da sabani a tsakaninsu. Aka yi auren ba tare da amincewar uban wannan dan uwan ba. Har ta kai ma sun kore shi daga gidan da suke zaune da shi. Me ya kamata wannan dan uwan ya yi kenan? A nan ya saba wa iyayensa ne da ya zama wajibi ya nemi gafararsu, ku kuwa ya abin yake?
Daga Muhammad Abuja
SHAIKH ZAKZAKY: Idan karama ce wadda ba ta balaga ba, waliccinta yana wajen ubanta da kakanta, kuma a wajenmu duk cikar su ikonsu daya a kan walicci din. Amma a bayanin da ya yi, ya ce ta isa aure, za mu kaddara yana nufin ta balaga ne, to a nan ita ce ta fi hakki fiye Mahaifinta da kuma kakanta. Saboda haka zabinta za a fifita, har ma in ma su biyun duka suka ki, ta samu ma ta wakilta wani ya daura mata aure, kuma auren ya yi. Illa iyaka in ta ba su waliccin din ta girmama su ne.
Amma tunda akwai rashin fahimta tsakanin uba da da a nan kamar yadda ya fadi, to sai shi dan ya yi kokari ya sasanta da Mahaifinsa, ya nuna masa cewa wannan a shari'ar Musulunci ma dai ita yarinyar ita take da hakki ba su ba, kuma bai kamata wannan ya zama sanadiyyar sabani a tsakaninsu ba, har dai ya shawo kansa su ci gaba da zumunci. Amma dai auren da ya yi, ya yi daidai.